Romans 12

1Ina rokon ku ‘yan’uwa, saboda yawan jinkan nan na Allah, da ku mika jikunanku hadaya mai rai, mai tsarki kuma abar karba ga Allah. wannan itace hidimarku ta zahiri. 2Kada ku kamantu da wannan duniya, amma ku sami canzawa ta wurin sabunta tunaninku, kuyi haka don ku san abin da ke nagari, karbabbe, kuma cikakken nufin Allah.

3Don ina cewa, saboda alherin da aka bani, ka da waninku ya daukaka kansa fiye da inda Allah ya ajiye shi; a maimakon haka ku kasance da hikima, gwargwadon yadda Allah yaba kowa bangaskiya.

4Domin muna da gababuwa da yawa a jiki daya, amma ba dukansu ne ke yin aiki iri daya ba. 5haka yake a garemu, kamar yadda muke da yawa haka cikin jikin Almasihu, dukkanmu gabobin juna ne.

6Muna da baye-baye dabam-dabam bisa ga alherin da aka bayar a gare mu. Idan baiwar wani anabci ne, yayi shi bisa ga iyakar bangaskiyarsa. 7In wani yana da baiwar hidima, sai yayi hidimarsa. Idan baiwar wani koyarwa ce, yayi koyarwa. 8Idan baiwar wani karfafawa ce, yayi ta karfafawa; Idan baiwar wani bayarwa ce, yayi ta da hannu sake; Idan baiwar wani shugabanci ne, yayi shi da kula; Idan baiwar wani nuna jinkai ne, yayi shi da sakakkiyar zuciya.

9Ku nuna kauna ba tare da riya ba. Ku Ki duk abin da ke mugu ku aikata abin da ke nagari. 10Akan kaunar ‘yan’uwa kuma, ku kaunaci juna yadda ya kamata; akan ban girma kuma, ku ba juna girma.

11Akan himma kuma, kada ku yi sanyi; akan ruhu kuma, ku sa kwazo; Game da Ubangiji kuma, ku yi masa hidima. 12Akan gabagadi kuma, ku yi shi da farin ciki; akan tashin hankali kuma, ku cika da hakuri; akan adu’a kuma, ku nace. 13Ku zama masu biyan bukatar tsarkaka, ku zama masu karbar baki a gidajenku.

14Ku albarkaci masu tsananta maku, kada ku la’anta kowa. 15Ku yi farinciki tare da masu farinciki; Ku yi hawaye tare da masu hawaye. 16Tunanin ku ya zama daya. Kada tunaninku ya zama na fahariya, amma ku yi abokantaka da matalauta. Kada wani a cikin ku ya kasance da tunanin yafi kowa.

17Kada ku rama mugunta da mugunta. Ku yi ayukan nagarta a gaban kowa. 18Ku yi duk abin da za ku iya yi domin ku yi zaman salama tare da kowa.

19‘Yan’uwa, kada ku yi ramako, ku bar Allah ya rama maku. A rubuce yake, ‘’ ‘Ramako nawa ne; zan saka wa kowa,’ in ji Ubangiji.‘’ 20‘’Amma idan makiyin ka na jin yunwa, ba shi abinci ya ci. Idan yana jin kishin ruwa, ba shi ruwan sha. Idan kun yi haka, garwashin wuta ne za ku saka akan duk makiyi.‘’ Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta ta wurin yin aikin nagarta.

21

Copyright information for HauULB